
Jarumar fim Kanyin Eros ta ce ya kamata a rika baiwa mata rol masu wuya kuma iri daban-daban kamar yadda a ke bawa maza a fina-finai.
Da ta ke magana da mujallar Sunday Scoop, ta ce, “Mata na iya zama komai. Su na iya buga rol din mugunta, jarumai, masu binciken laifuka. Duk wata rawar da za a iya ba wa maza kuma za a iya ba wa mata. Mu ma za mu iya yi.”
Ta bayyana cewa ya kamata masana’antar ta kasance a buɗe kofa ga mata da yawa su rika hawa rol daban-daban fiye da irin wanda aka saba basu na iyaye, kwalliya da sauransu.
“Masana’antar tana da wahala. Akwai mata masu hazaka da yawa a wajen, amma bana jin akwai isassun ayyuka da ake basu,” inji ta.