
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga dadi ne, sun budewa tsohon sakataren gwamnatin Filato wuta, inda suka harbe shi har lahira.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a wata wasika da aka rabawa manema a labarai, a Jos babban birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Filato Terna Tyopev ya ce, da misalign karfe 9 na daren ranar talata ne, ‘yan bidigar su ka budewa Moses Gwom wuta a kofar gidansa, da ke yankin karamar hukumar Barikin Ladi, inda nan take yace ga garinku nan.
Maharan sun kuma bude wuta ga wasu mutum 12 a lokacin da suka kai wannan hari, yayin da damansu suke cikin wani mawuyacin hali.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ya zuwa yanzu babu wasu mutane da ake tsare dasu kan wannan hari, amma suna nan suna gudanar da bincike.