Home Labarai ‘Yan Kwankwasiyya na cigaba da bijirewa zabin Kwankwaso a takarar Gwamnan Kano

‘Yan Kwankwasiyya na cigaba da bijirewa zabin Kwankwaso a takarar Gwamnan Kano

0
‘Yan Kwankwasiyya na cigaba da bijirewa zabin Kwankwaso a takarar Gwamnan Kano

Magoya bayan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso karkashin Kwankwasiyya sun bijirewa zabin da Kwankwaso yayi na kakaba sirikinsa a matsayin wanda zai shiga takara a PDP daga bangaren ‘Yan Kwankwasiyya.

Da yawan jiga jigan kungiyar Kwankwasiyya sun nuna damuwa akan wannan zabi da Kwankwaso yayi na nuna sonkai da fifita bukatarsa akan ya mabiyansa da suka sha wahala tare da shi a siyasance.

Daga cikin makusantan Sanata Kwankwaso da suka bijirewa wannan zabin nasa akwai Injiniya Muazu Magaji Wanda ya nuna rashin gamsuwa da wannan zabi a shafinsa na Facebook.

Da yawan magoya bayan Kwankwaso a kafafen sada zumunta na intanet na nuna bijirewarsu akan wannan zabin na Kwankwaso inda yake kakaba surikansa akan dukkan wasu manyan mukamai ko kujeru.