Home Labarai Yan majalisar dokoki 27 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Jihar Rivers

Yan majalisar dokoki 27 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Jihar Rivers

0
Yan majalisar dokoki 27 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Jihar Rivers

Kimanin ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa jam’iyyar APC.

Ƴan majalisar sun bayyana ficewarsu ne a wani hoto, inda aka gansu rike da tutar jam’iyyar APC.

Sun bayyana rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP a matsayin dalilin farko na ficewarsu.

Wannan ci gaban ya kara dagula rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da ‘yan majalisa masu biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike.