
Hassan Y.A.Malik
Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya yi bayani kan lokacin da uban gidan nasa zai kai ziyarar jaje ga gwamnatin Yobe, iyayen yaran da aka sace da ma makarantar gwamnati ta Dapchi inda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da ‘yan mata 111 a daren Litinin din da ta gabata.
Mista Adesina ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, inda a lokacin da mai gabatar da shirin ya tambaye shi lokacin da shugaban kasa zai ziyarci Yobe, sai ya kada baki ya ce “Shugaba Buhari shi ne shugaban Nijeriya kuma zai ziyarci Yobe ne a lokacin da ya ga dacewar hakan.”
Ya ci gaba da cewa, babu wani dalili da zai saka Buhari ya ziyarci Yobe a halin yanzu tunda ya tura tawaga har guda biyu don ta yi masa wakilci kana kuma ta zo masa da rahoton yadda abubuwa suka kasance a Dapchi.
“Bai kamata a ce saatr ‘yan mata ya sake faru ba a makaranatrsu a nan kasar bayan faruwar na ‘yan matan Chibok. Amma tunda hakan ta faru, gwamnati ta shiga aiki babu dare babu rana wajen kiyaye farun hakan a nan gaba.”
“Ina rokon iyayen yaran da aka sace da su yi wa gwamnati hakuri, kuma su amince cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta dawo musu da yaransu.”
“Shugaban kasar Nijeriya shi ne uban Nijeriya kuma zai iya ziyartar duk inda ya ke so ya ziyarta a duk lokacin da ya ke son hakan.”
“Tawagar da ya tura Yobe za ta zo masa da kammalallen rahoto, wannan zai tabbatar da bukatar zuwansa ko a’a,” inji Mista Adesina
Gwamnatin tarayya dai ta tabbatar da cewa ‘yan mata 110 ne na makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati da ke Dapchi a jihar Yobe sun bata.