Karamin jakadan Najeriya dake birnin Guangzhou a kasar Chana Wale Ploko, a ranar litinin ya bayyana cewar ‘yan najeriya da yawa ne suke garkame a kurkuku da dama a birnin Guandong sabida wuce ka’idar lokacin da ya kamata su zauna a kasar.
Mista Oloko ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na najeriya, NAN, cewar, bayan haka kuma, ana tsare da ‘yan najeriya da yawa akan lafukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da sauran laifuffukan da suka aikata a kasar.
A cewarsa, yanzu haka akwai sama da ‘yan Najeriya 600 da ake tsare da su sabida zarta lokacin da aka basu na zama a kasar da suka yi.
“Babu ko tantama ceewar ‘yan najeriyar da ke garkame a gidajen yarin kasar Chana suna da yawa kwarai da gaske.”
“Suna nan jibge a gidajen yarin kasar, sabida laifuffuka daban daban da suka aikata”
Mista Oloko ya bayyana cewar wasu daga cikin ‘yan najeriyar da ake tsare da su a gidajen yarin kasar ana shirin dawo da su gida Najeriya.
A sabida haka ne, karamin jakadan yayi kira ga ‘yan najeriya da su kasance masu kiyaye dokokin kasar Chana a duk inda suka shiga a kasar, musamman jami’an shige da fice na kasar Chana.
“Duk dan Najeriyar da yake son ziyartar wasu sassan kasar Chana, ya tabbatar ya tafi da dukkan takardun Shaida, sannan ya kaucewa dukkan wani abu na kayan laifi da zasu iya sanyawa a kama su”
Guandong wani yanki ne a kudancin kasar Chana, wanda ke kusa da tekun dake kudancin kasar Chana.
NAN