Home Labarai ‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa wani gungun ‘yan fashi da suka addabi jama’a

‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa wani gungun ‘yan fashi da suka addabi jama’a

0
‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa wani gungun ‘yan fashi da suka addabi jama’a

Daga Hassan AbdulMalik

Rundunar ‘yan Sandan birnin tarayya Abuja ta bayyana kama wani gungun ‘yan fashi da makami da suka dade suna addabar rukunin gidaje na gwamnatin tarayya mai suna Sauka Federal Housing Area.

Majiyarmu ta bayyana cewa ‘yan fashin da adadinsu ya kai 30 na tsaka da yin fashi akan hanya ne a lokacin da ‘yan sanda suka samu kiran yawa cewa akwai ‘yan fashi akan hanya, inda nan take suka garzaya wajen.

Da isar ‘yan sandan ne fa sai suka shiga artabu da ‘yan fashin, inda a nan take ‘yan sanda suka harbe ‘yan fashi biyu suka mutu, uku kuma suka tsere da raunika, inda aka cafke wasu ukun.

An samu ‘yan fashin da bindigu kirar Hausa, talabijin na bango guda 9, takalma da kuma wuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Manzah Anjugri ya tabbatar da faruwar wannan labari, inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bawa ‘yan sanda hadin kai don kawar da masu laifi a fadin birnin tarayya Abuja.

Manzah ya ce, “A wani fita aikin da muka yi ma mu n kama wasu mutum shida a yankin Banex a lokacin da muke caje ababen hawa. Mun yi nasarar kwato bindigu da tabar wiwi daga hannunsu. Za mu ingiza keyarsu zuwa sashen bincike na hukumarmu don gudanar da bincike akansu.”