
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta cafke wasu mutane 11 wadanda ake zargi da haddasa rikicin da ya barke a tsakanin wasu kauyuka 2 Katch/Kpata Kacha a karamar hukumar Mokwa a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr. Dibal Yakadi, ya tabbatar da cafke wadannan mutane a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) yau Laraba, a garin Minna.
Kwamishinan ya ce rikicin ya barke a yankin ne sakamakon fada da ya barke a tsakanin wasu ‘yan uwa wadanda kowane daga cikin su ya kasance daga kauye daban wanda sanadiyyar hakan ne ya haddasa barkewar rikici tsakanin kauyukan 2.
Mutum 1 ne ya rasa ransa sakamakon rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa fuloti (fili) ne ya haddasa fada a tsakanin ‘yan uwan.
Kwamishinan ya fadawa NAN cewa rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta aika jami’an tsaro 70 zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya a kauyukan.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su taimakawa jami’an tsaro da duk wani bayani wanda zai taimaka masu wajen gudanar da binciken su.