Home Labarai ‘Yan sanda sun hana yin zanga zangar Allah wadai da Ganduje a Kano

‘Yan sanda sun hana yin zanga zangar Allah wadai da Ganduje a Kano

0
‘Yan sanda sun hana yin zanga zangar Allah wadai da Ganduje a Kano

A ranar Laraba wasu kungiyoyin dalibai suka shirya yin wani jerin gwano daga titin gidan namun daji a cikin birnin Kano zuwa fadar Gwamnatin jihar domin yin Allah wadai da halin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje kan badakar cin hanci da aka nuna shi yana karba a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Sai dai kuma, rundunar ‘Yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta gargadi kungiyoyin daliban da kada su kuskura su fito zanga zanagar a cewarsu, ba a basu iznin gudanar da wannan jerin gwano ba.