
Kwamishinan Ƴan Sanda a Jihar Enugu, Lawal Abubakar, ya ce a ƙalla mutane 46 ne a ka kama bisa laifuka daban-daban tsakanin watan Maris zuwa Afrilu a jihar.
An kama su da laifuffuka daban-daban da su ka haɗa da haɗa baki, kisa, fyaɗe/kazanta, garkuwa da mutane, fashi da makami, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, sata, barna da ƙungiyar asiri.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan, ASP Daniel Ndukwe, ya rabawa Kamfanin Dillancin Labarai labarai na Ƙasa, NAN a Enugu a yau Juma’a.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, an samu nasarar ceto mutane huɗu da a ka yi garkuwa da su, tare da ƙwato bindigogi 25 masu samfuri daban-daban da kuma harsasai 31 masu girma daban-daban.
Ya ce sauran kayayyakin da aka kwato sun haɗa da harsashi masu rai guda 53, motoci uku, babura uku guda shida, babura biyu da sauran ababen da ba a taba gani ba.
Ya yaba da goyon bayan da aka samu daga masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, wanda ya ce hakan ne ya sa aka samu nasarar gudanar da ayyukan a jihar.
Ya ce al’umma a jihar za su iya bayar da rahoto ta hanyar kiran layukan gaggawa na rundunar ta: 08032003702, 08075390883 ko 08086671202, ko kuma ta adireshin contact042ppro@gmail.com