Home Labarai Yan sanda sun kama sojan ruwa na ƙarya a Nasarawa

Yan sanda sun kama sojan ruwa na ƙarya a Nasarawa

0
Yan sanda sun kama sojan ruwa na ƙarya a Nasarawa

 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta cafke wani jami’in sojan ruwa na bogi a jihar.

DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya bayyanawa manema labarai a yau Asabar a garin Lafiya.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, an kama wanda ake zargin sanye da cikakken kakin soja da kuma katin shaidar aiki mai ɗauke da sunansa.

“A ranar 25 ga Agusta, 2022, an kama wani mutum mai shekaru 33, dan asalin Ƙaramar Hukumar Nassarawa-Eggon, sanye da kakin sojoji.

“Wanda ake zargin, wanda ya yi ikirarin yana aiki a jihar Kogi, an kama shi ne a kasuwar Doma da cikakken kakin Sojoji. Jami’an runduna ta 4 na musamman a Doma ne su ka kama shi tare da mika shi ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike,” inji shi.

Kakakin ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya sayo kayan aikin soja ne daga jihar Legas.

Jami’in a cikin sanarwar, ya kara da cewa wanda ake zargin ya dade yana sanyawa domin yaudarar jama’a da ba su ji ba, kafin karyarsa ta kare.

Ya ci gaba da cewa binciken ya kai ga kwato wasu kayayyakin aikin sojin ruwan Najeriya.

Ya zayyano kayan kayan da suka hada da gajerun wanduna guda biyu, wuka, katunan shaida guda biyu na sojojin ruwan Najeriya masu dauke da sunan wanda ake zargin, nelt, wayoyin hannu guda biyu da sauran su.