
Daga Hassan Y.A. Malik
Hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta maka Sanata Dino Melaye a gaban wata kotun majistare mai zamanta a Wuse 2, Abuja.
Sanatan da a halin yanzu ke karbar kulawa daga jami’an lafiya na babban asibin tarayya da ke birnin Abuja sakamakon tsalle da ya yi ya diro daga motar ‘yan sanda a makon da ya gabata, an kawo shi gaba alkalin majistaren a kan gadon asibiti.
‘Yan sandan sun gurfanar da Dino ne bisa zarginsa da hannu a aikata mugun laifi
Zuwa lokacin da muka hada wannan rahoto, kotu ta ki baiwa ‘yan jarida damar shiga dakin shari’ar.
Za mu kawo yadda ta kaya…