Home Labarai ‘Yan sanda sun tarwatsa Kwankwaso da magoya bayansa a Kano

‘Yan sanda sun tarwatsa Kwankwaso da magoya bayansa a Kano

0
‘Yan sanda sun tarwatsa Kwankwaso da magoya bayansa a Kano

A ranar Litinin din nan be rundunar ‘Yan sanda ta jihar Kano ta tarwatsa Kwankwaso da gungun magoya bayan Kwankwasiyya a jihar Kano yayin da Sanata Kwankwaso ya zo Kano a karon farko cikin shekaru uku a kokarinsa na karbe ikon ragamar gudanar da jam’iyyar PDP a jihar Kano.

An tsara Sanata Kwankwaso tare da ‘Yan tawagarsa zasu kaddamar da sabon Shugabancin jam’iyyar karkashin Rabiu Sulaiman Bichi da Kwankwaso yayi karfa karfa wajen basu ikon jam’iyyar.

Sai dai kuma, tun a wancan lokaci kotu ta yi hukunci inda ya nemi kada a rushe Shugabancin PDP karkashin Sanata Masud el-Duguwa. Mai Shariah N Umar inda ya nemi da kada a yi wani duk wani yunkuri na rushe Shugabancin PDP din karkashin Doguwa.

I