Home Labarai ‘Yan takarkaru 300 sun fice daga APC a jihar Kano

‘Yan takarkaru 300 sun fice daga APC a jihar Kano

0
‘Yan takarkaru 300 sun fice daga APC a jihar Kano

A jihar Kano Akalla ‘Yan takarkaru 300 ne suka bayyana ficewar su daga jam’iyyar APac mai mulkin jihar bayan da da yawansu suka fadi zaben fidda gwani na jam’iyyar da suka bayyana cewar anyi rashin adalci a cikinsa.

Sanata Isa Yahaya Zarewa wanda yayi takarar majalisar dattawa a yankin Kano ta kudu yana daya daga cikin mutanan da suka fice daga APC din yana mai bayyana rashin gaskiya da aka nuna musu a yayin zaben fidda gwani da aka yi a jam’iyyar.

Sanata Zarewa a zantawarsa da manema labarai a ranar Litinin ya bayyana cewar Sam ba zabe aka yi ba a jihar Kano, Gwamnati ce kawai ta rubuta abinda taga dama.

Ya Kara da cewar sun rubuta koke zuwa ga uwar jam’iyyar domin daukar mataki amma ba abinda tayi dan yiwa ‘Yan jam’iyyar Adalci da aka zalinta.

’Yan takarkaru a kujerun sanata da na majalisar wakilai ta masa da majalisun dokoki na jiha ne dai suka bayyana ficewarsu daga cikin jam’iyyar ALC mai mulki.