Home Labarai Yanayin zafi ya sanya matan Abuja cire ƙarin-gashi da yin aski

Yanayin zafi ya sanya matan Abuja cire ƙarin-gashi da yin aski

0
Yanayin zafi ya sanya matan Abuja cire ƙarin-gashi da yin aski

Yayin da yanayin zafi ke daɗa tsamari har ya kai digiri 40 a ma’aunin celcius, mata da dama a Abuja na ta cire ƙarin-gashi da kuma yin aski don su sha iska.

Ga wasu matan, su na amfani da ƙarin-gashi a matsayin ado amma na lokaci zuwa lokaci kuma za su iya rayuwa ba tare da shi ba.

Sai dai kuma Titilope Ariyo, wata ƴar kasuwa, ta ce duk da cewa mijin ta ya hana ta aske gashin kanta, amma dole ta cire ƙarin-gashi ta kuma yi askin saboda yanayin zafi.

“Hakika ya yi min barazanar cewa zai kore Ni gida idan na yi aski saboda bai yarda mata su yi aski ba, amma na yi hakan ne saboda ina bukatar iska a kai na

“Na yi alkawari cewa zan sake fito da gashin idan zafi ya wuce.

Ita kuwa Joy Kaka, ƴar jarida, ta ce ta yi aski ne a wani mataki na gyaran gashin ta da yanke ta zube wa.

Duk da haka, yanke shi a lokacin zafi ya kasance shawara mai kyau kamar yadda ya dace da bukatarta don magance yanayin zafi.

“Na yanke gashin kaina ne saboda yana ta zubewa ne kuma na yanke shawarar na far barin shi ya tofo amma na fuskanci zan ci gaba da sake shi ya zu saboda yanayi. Ina jin dadin zuba ruwa a kaina.

Da yake magana game da tasirin zafi a kan kiwon lafiya, Dr Henry Ewunonu, likita kuma mai ba da shawara kan kiwon lafiya, ya dora alhakin lamarin kan sauyin yanayi.

Ya ce hakan ya faru ne saboda mutane sun lalata fatar ozone wacce a halin yanzu ke da ƙofofi kuma hakan ya sanya zafin rana ke wucewa ya samu duniya.

Ya ce dan Adam na lalata fatar ozone din ne ta hanyar kona man fetur da sauran abubuwan da ba su dace ba da suka shafi yanayin yanayi kamar sare dazuzzuka da kuma tara shara barkatai.