
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da bullar cutar ƙyandar biri a yau talata.
Sanarwar ta zo ne bayan da a ke zargin mutane uku sun kamu da cutar a jihar, kamar yadda Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana wa manema labarai a yau Talata a Gombe.
Dahiru ya ce daga cikin samfurin mutane 19 da ake zargin sun kamu da cutar da aka kai ma’aikatar lafiya ta jihar domin gwaji, an gano guda uku na dauke da cutar.
A cewar sa, mutanen guda uku da aka gabatar sun ce suna fama da zazzabi wanda ya dauki sama da mako guda duk da maganin kashe zazzabi da su ka sha.
Ya kara da cewa alamun cutar ma ta nuna a fuskokinsu da sauran sassan jikinsu, wanda hakan ya sa ake zargin cutar kyandar biri.
Ya kara da cewa, “Bisa la’akari da abubuwan da suka faru a sama, na sanar da bullar cutar kyandar biri a jihar Gombe.”
Dahiru, ya ce dukkan mutane ukun da aka tabbatar sun kamu da cutar tun daga lokacin an duba su da basu magani kuma an sallame su daga asibiti.