
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, shiyyar Maiduguri, ta samu nasarar kotu ta yanke wa Aisha Wakil, wacce q ka fi sani da Mama Boko Haram hukunci tare da wani Tahiru Alhaji, Saidu Daura da kuma Yarima Lawal Shoyode.
Mai shari’a, Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno ce ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, bisa samunsu da laifin haɗa baki da kuma wasu shekaru bakwai saboda samun kudi ta hanyar zamba-cikin-aminci.
Kafin a yanke masu laifin, an fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar 14 ga Satumba, 2020 a gaban Mai shari’a Kumaliya, bisa laifuka biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma karbar kudi ta hanyar zamba-cikin-aminci da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.
Wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, wanda hakan ya sa lauya mai shigar da kara, Mukhtar Ali Ahmed ya gabatar da shaidu shida tare da gabatar da wasu takardu a matsayin shaida a gaban kotu, sannan ya rufe kararsa a ranar 27 ga Oktoba, 2020.
Da ta ke yanke hukuncin, Mai shari’a Kumaliya ta samu wadanda ake tuhumar da laifuka biyu da ake tuhumarsu da aikatawa, tare da yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai kowanne ba tare da zabin biyan tara ba kan laifin hada baki.
Alkalin ta ƙara da yanke musu hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari ba tare da zabin tara kowannensu a bisa laifin samun kudi ta hanyar zamba-cikin-aminci.
Ya kuma umurci wadanda aka yankewa hukuncin da su hada kai su dawoda kudin da su ka karɓa, Naira miliyan 15 ga wadanda su ka karɓe wa kuɗaɗen, inda ya ce kin yin hakan ka iya sanya wa su kara daurin shekaru biyar a gidan yari.
A baya dai Mai shari’a Kumaliya ta yanke wa “Mama Boko Haram” hukuncin daurin shekaru biyar a kan laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma karbar sama da Naira miliyan 71 ta hanyar zamba-cikin-aminci.
An daure ta a ranar 15 ga Yuni, 2022.