Home Labarai An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu a kan dukan maƙwabciya

An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu a kan dukan maƙwabciya

0
An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu a kan dukan maƙwabciya

 

Alkalin Kotun Majistare, Ibrahim Emmanuel a yau Alhamis ya umarci wata matar aure mai suna Hadiza Ahmed da ta share harabar kotun na tsawon kwanaki biyar saboda ta yi wa makwabciyar ta duka.

Emmanuel, ya ba da umarnin ne biyo bayan amsa laifin da Hadiza Ahmed ɗin ta yi.

“An umarce ki da ki share tare da tsaftace harabar kotun nan na tsawon kwanaki biyar a karkashin bibiyar magatakardan kotun.

“Hukuncin zai zama izina ga wasu da ba sa son zaman lafiya da maƙwabta,” in ji shi.

Tun da fari dai, Lauyan masu shigar da ƙara, Sifeto Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa Hadiza ta aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Maris a Tudun Wada, Kaduna.

Leo ya ce ba tare da wata tsokana ba, Hadiza ta buɗe baki ta zagi mai korafin, Farida Musa, inda hakan ya mai su ga faɗa.

Ya ƙara da cewa, a yayin faɗan, wacce a ke ƙara ta lakaɗa wa mai ƙarar dukan tsiya.

Laifin, a cewar sa ya saɓawa tanadin sashe na 173 na kundin laifuffuka na Jihar Kaduna na 2017.