Home Labarai An yanke wa ƴan vigilante 5 daurin rataya bisa kashe wani matashi a Kano

An yanke wa ƴan vigilante 5 daurin rataya bisa kashe wani matashi a Kano

0
An yanke wa ƴan vigilante 5 daurin rataya bisa kashe wani matashi a Kano

Babbar kotu a jihar Kano, karkashin alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta yanke wa wasu ƴan vigilante biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wani matashi mai suna Ahmad Musa (Khalifa) dan shekara 17 a Sabon Titin Panshekara a jihar Kano.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Emmanuel Korau, Eliesha Ayuba Jarmai, Irimiya Timothy, Auwalu Jafar da Mustapha Haladu.

An same su da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma kisan kai wanda ya saɓawa sashe na 97 da 221(b) na dokar Penal Code.

Wadanda aka yankewa hukuncin dai sun musanta laifin da ake tuhumar su da su.

Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu biyar don tabbatar da tuhumar da ake musu, yayin da lauyan wadanda ake kara, Barista Ahmad Muhammad, ya gabatar da shaidu shida ciki har da wadanda ake karar

Sai dai alƙaliyar ta yanke cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjojin su ba tare da wata shakka ba, don haka ta yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin da ya dace.

Tun da fari, lauyan masu shigar da kara, Barista Lamido Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Junairu, 2022, wadanda aka yanke wa hukuncin, wadanda ‘yan kungiyar ’yan vigilante ne da ke cibiyar matasa ta Sani Abacha, suka hada baki tare da kaiwa marigayi Ahmad Musa hari, a Sabon Titi.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi amfani da wata doguwar sanda (gora) inda suka yi wa mamacin duka da shi, sannan wanda ake kara na farko ya yi amfani da wuka ya daba wa marigayin a wuya.

Daga baya ne suka dauki gawar marigayin a cikin babur mai ƙafa uku zuwa ofishinsu.

Daga baya an kai marigayin zuwa sashin ‘yan sanda na Kuntau inda aka garzaya da shi asibiti.

Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.