
Kotun Spain ta Ƙasa ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin yin barazanar kashe Firaministan Spain, Pedro Sanchez.
Manuel Murillo, mai shekaru 66, ya wallafa sakonni a shafukansa na sada zumunta da kalaman barazana ga Sanchez.
Ƴan sanda sun kai sumame gidan Murillo kuma sun kama haramtattun makamai guda bakwai, ciki har da bindiga mai sarrafa kanta.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Murillo ya yanke cewa mutuwar Firaministan ita ce kaɗai mafita don kawo sauyi a siyasar Spain.
Alkalan sun kuma ce makaman da aka kama a wajen Murillo na nuni da cewa akwai hatsarin gaske.