Home Labarai Da ga yanzu ba wanda zai ga Buhari sai an yi masa gwajin korona — Garba Shehu

Da ga yanzu ba wanda zai ga Buhari sai an yi masa gwajin korona — Garba Shehu

0
Da ga yanzu ba wanda zai ga Buhari sai an yi masa gwajin korona — Garba Shehu

 

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za a riƙa yi wa duk wani baƙo da zai shiga fadar shugaban ƙasa gwajin korona kafin a ba shi izinin shiga.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Lahadi.

Ya ce an tanadi kayan gwaje-gwajen korona cikin sauri waɗanda za su baiyana sakamakon cikin ‘yan mintuna kaɗan a gani ko mutum ya na ɗauke da cutar ko bashi da ita.

A cewar Garba Shehun, sabuwar dokar ta zama dole sabo da ƙaruwar adadin masu kamuwa da cutar, musamman nau’in Omicron a duniya.

“Eh, an sanya sabon tsarin dokar gwajin korona ne ga duk masu ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa. Amma badon gwamnoni kadai ba, kowane mai ziyara a fadar shugaban ƙasa, ba kawai wadanda ke ganin shugaban kasa ba. Yanzu a na buƙatar yin gwajin gaggawa a kofar gidan kafin a shiga don gudun yaɗa cutar a fadar shugaban ƙasar,” in ji Garba Shehu.