Home Kanun Labarai YANZU-YANZU: Ƴan ta’adda sun ɗauke mutane 18 a Kaduna

YANZU-YANZU: Ƴan ta’adda sun ɗauke mutane 18 a Kaduna

0
YANZU-YANZU: Ƴan ta’adda sun ɗauke mutane 18 a Kaduna

 

Rahotanni sun baiyana cewa a ƙalla mutane 18 ne, har da mata ƴan ta’adda su ka yi garkuwa da su a Angwar Zalla Udawa a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.

Rahotannin sun baiyana cewa ƴan ta’addan kuma sun bindige mutum ɗaya.

An ce ƴan ta’addan sun dira a garin ne wanda ya ke kan hanyar Kaduna zuwa Barinin Gwari da misalin ƙarfe 12:30 na safe a yau Lahadi.

Wani sannen mutum a garin Udawa, Muhammad Ummaru ya tabbatar da cewa an kashe mutum ɗaya mai suna Bala Jaja.