
Binta Nyako, Alkaliyar babbar kotun tarayya ta janye daga zaman sauraron karar da ake tuhumar jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamadi Kanu.
Alkalai dai sun saba janye wa daga sauraron shari’a saboda zargin son rai ko nuna bangaranci.
A yayin zaman kotun a yau Talata, Nnamadi Kanu ya shaidawa Alkaliyar cewa bashi da kwarin gwiwa kan ta game da shari’ar, mai yiwuwa shi ne dalilin da ya sa ta janye.