
Rahotanni sun daga jihar Sakkwato na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe dansanda daya da wani dan bijilante da ke kan sintiri a jihar.
Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3 na asubar yau Litinin a Kwanar Milgoma da ke kan titin Sakkwato zuwa Bodinga.
Duk da cewa Daily Trust ba ta samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wani babban jami’in ‘yan sandan da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa wakilin ta harin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi wa jami’an tsaron kwanton-bauna ne a cikin wata farar mota kirar Hilux.
“Ƴan bindigar sun hadu da ƴansandan ne a wani shingen bincike da ke kan hanyar Sakkwato zuwa Bodinga inda suka bude musu wuta. Sun kashe dan sanda daya da dan banga sannan suka tafi da bindigogi kirar AK-47 guda biyu.
“An ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo,” inji shi