Home Kanun Labarai YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun sace ɗan takarar gwamna a Filato

YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun sace ɗan takarar gwamna a Filato

0
YANZU-YANZU: Ƴan bindiga sun sace ɗan takarar gwamna a Filato

 

Yan bindiga sun ɗauke ɗan takarar gwamna a jam’iyar PDP a Jihar Filato a zaɓen 2019, Kemi Nicholas Nshe.

Rahotanni sun baiyana cewa an ɗauke Nshe tare da wani malami a Jami’ar Filato, Monday Hassan a ranar Asabar.

Satar Nshe da Hassan ta zo ne kusan mako ɗaya bayan da ƴan bindiga su ka yi garkuwa da Sum Pyem, Charles Mato Dakat a fadar sa da ke Gindiri, Ƙaramar Hukumar Mangu.

Kakakin Rundunar Ƴan Sanda na jihar, ASP Gabriel Uba bai yi magana a kan harin ba dai kawo yanzu.