
A yau Lahadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a garin Daura na jihar Katsina, ya amince da tsawaita wa’adin kwanaki 10 na musayar kudade zuwa sabbin takardun kudi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ruwaito cewa Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan a garin Daura na jihar Katsina, ya bayyana cewa sabon wa’adin ya kasance 10 ga watan Fabrairu.
Emefiele, wanda ke Daura a safiyar yau Lahadi, ya yi ganawar sirri da Buhari, inda ya samu amincewar sa.
Ya ce ’yan Nkjeriya, wadanda har yanzu ba su canza takardar kudin Naira daga tsohuwar zuwa sababbi ba, “yanzu suna da damar yin hakan”.
Gwamnan babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne mutane su yi amfani da damar nan domin ba za a sake tsawaita wa’adin ba.