
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sha kaye a yunkurin sa na komawa mulki karo na biyu a jihar Zamfara.
Dauda Lawan Dare, dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, shi ne ya lashe zaɓen da tsira ƙuri’u 65, 750.
Jami’in zaɓen, Kasimu Shehu, da ya ke sanar da zaɓen, ya ce Dare ya samu ƙuri’u dubu 377,726, inda Matawalle ya samu ƙuri’u dubu 311, 976.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Matawalle ya zama gwamnan Zamfara ne a zaɓen 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.