
A yammacin Alhamis ɗin nan ne dai jami’an Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC su ka damƙe Gwamnan Jihar Anambra mai barin-gado, Willie Obiano a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
A cewar sahfin yanar gizo na Channels TV, an kama Obiano ɗin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a yau.
Obiano, wanda a yau rigar kariyar sa daga kame ta ƙare, ya kasance a cikin jerin sunayen waɗanda EFCC ɗin ke fako.
Rahotanni sun baiyana cewa an cafke Obiano ne yana kan hanyar sa 5w zuwa Houston, a Jihar Texas da ke Amurka.
Ƙarin bayani na nan tafe…