Home Labarai YANZU-YANZU: An kama telan dake ɗinka tutar Russia da masu zanga-zanga ka ɗaga wa a Kano

YANZU-YANZU: An kama telan dake ɗinka tutar Russia da masu zanga-zanga ka ɗaga wa a Kano

0
YANZU-YANZU: An kama telan dake ɗinka tutar Russia da masu zanga-zanga ka ɗaga wa a Kano

Jami’an tsaro sun kama ɗaya daga cikin masu hannu a yaɗuwar tutar ƙasar Russi a yayin zanga-zanga a Kano.

Daily Trust ta rawaito cewa, dubban matasa da ke zanga-zangar matsin rayuwa sun daga tutar Russia a wasu sassa a fadin ƙasar a yayin zanga zangar.

Lamarin ya fara ne kadan-kadan a kwanakin baya, inda daga baya ga fara ɗaukar hankali bayan da ya fantsama zuwa jihohi a yau Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Tinubu ya gargadi masu zanga zangar kan kada a yi amfani dasu wajen kifar da gwamnatin sa.

A yau Litinin, ƴansanda sun kama Telan dake dinka tutar da masu amfani da ita.

Telan mai suna Ahmed, an kama shi da yadika na tutar kasar ta Russia.

A yanzu haka dai ya na tsare a hannun hukumar yansanda a jihar Kano inda ake masa tambayoyi.