
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC ta sanar da sauya ranar gudanar da zaben kananan hukumomi zuwa 26 ga watan Oktoba.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, tun da farko hukumar ta sanya ranar 30 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben.
A yayin taron manema labarai a yau Juma’a a Kano, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya ce an dau matakin ne duba da hukuncin da kotun koli ta yi na bai wa kananan hukumomi ‘yanci.
“Duba da hukuncin kotun koli tayi na kwanan nan da kuma yarjejeniyar fahimtar juna da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kasancewar watan Oktoba ya zama na karshe na baiwa kananan hukumomi yancin kansu, wannan hukuma na sake fitar da jadawalin zaben kananan hukumomi zuwa 26 ga watan Oktoba, maimakon 30 ga watan Nuwamba, 2024.
” Wannan hukuma na neman masu ruwa da tsaki dasu fahimci yanayin kuma su baiwa hukumar goyan bayan da yakamata”.
Malumfashi, ya ce bisa gyaran da aka yi, a yanzu za a fara yakin neman zabe daga 1 ga watan Satumba zuwa karfe 12 na daren 26 ga watan Oktoba.
Sannan ya kara da cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu daga 3 ga watan Satumba zuwa 26 ga watan.
Sannan ya kara da cewa za a sanar da sakamakon zabe a ranar Lahadi 27 ga watan Oktoba.
Haka kuma, hukumar ta ware ranar 9 ga watan Nuwamba domin zaben cike gurbi idan akwai bukatar hakan.