
Wata babbar kotun jihar Kano, karkashin jagorancin Mai shari’a Amina Aliyu ta hana ƴansanda, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS da sojojin Najeriya daga fitar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar sarki.
Sarkin ya shigar da karar ne tare da masu naɗa Sarki su hudu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan and; Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.
Da ta ke bayar da wannan umarni, Mai shari’a Aliyu ta kuma hana jami’an tsaro kamawa ko muzgunawa Sarkin da masu naɗa Sarkin.
An daga zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2024 don sauraren karar.