Home Labarai YANZU-YANZU: Majalisar dokoki ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan 10

YANZU-YANZU: Majalisar dokoki ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan 10

0
YANZU-YANZU: Majalisar dokoki ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan 10

 

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amincewa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ciyo bashin naira biliyan goma.

Freedom Radio ta rawaito cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da za a ciyo bashin ne wajen sanya na’urorin kyamarorin tsaro, wacce a ka fi sani da CCTV domin kyautata tsaro a jihar.

Amincewar ciyo bashin ta biyo bayan wasiƙar da gwamnan ya aikewa majalisar wadda shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.

Ta cikin wasiƙar gwamna Ganduje ya ce, za a sanya na’urorin ne la’akari da barazanar tsaro da jihar ke fuskanta a ƴan kwanakinnan.

Wakilin Freedom Radio a majalisar ya ruwaito cewa, bayan tattauna batun ne tare da bada shawarwari ƴan majalisar suka amince a ciyo bashin.