
Mawaƙi Ali Jita ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Ibrahim Jibrin, kamar yadda Freedom Radio ta rawaito.
Jita dai na cikin jiga-jigan ƴan Kwankwasiyya daga masana’antar fina-finan Hausa, inda shi ne ya yi fitacciyar waƙar nan ta ‘Abba Gida-gida Abba ne…’.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Barau ke ci gaba da yiwa darikar Kwankwasiyya ɗauki-ɗai-ɗai duk da cewa su suke da gwamnati a hannu a jihar Kano.
Freedom ta tuna cewa ko a kwanakin baya ma Sharu Habu Tabule da Rabi’u Daushe sun fice daga Kwankwasiyyar zuwa APC gidan Barau.
A gefe guda kuma ana ta samun masu kokawa da tsarin da ƴan Kannywood na Kwankwasiyya ke ciki, kamar su Jarumi Garzali Miko da Jaruma Hafsat Muhammad da Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya fina-finai ta Ƙasa Malam Salisu Officer sun fito sun koka.