Home Labarai YANZU-YANZU: Ngelale ya ajiye aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu

YANZU-YANZU: Ngelale ya ajiye aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu

0
YANZU-YANZU: Ngelale ya ajiye aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu

Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, Chief Ajuri Ngelale ya ajiye aiki sakamakon rashin lafiya.

Ajuri, ya bayyana hakan ne a wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

“A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, inda na ke shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiya wanda hakan abun damuwa ne ga ahali na.

” A yayin da na ke godiya kan wannan nauyi da aka dora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai kuma mai magana da yawunsa; jakada na musaaman ga shugaban kasa a fannin sauyin yanayi kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan shirin Evergreen.

“Na dau wannan matakin ne bayan tuntubar iyalina a yayin da rashin lafiya ya tsananta a gida na.

Zan dawo bakin aiki da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama,” in ji Ngelale.