Home Labarai YANZU-YANZU: NNPC ya kara farashin litar mai zuwa N904 a Kano

YANZU-YANZU: NNPC ya kara farashin litar mai zuwa N904 a Kano

0
YANZU-YANZU: NNPC ya kara farashin litar mai zuwa N904 a Kano

Farashin man fetur a jihar Kano ya kai Naira 1,200 a wasu gidajen mai yayin da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya daidaita farashinsa zuwa Naira 904 kowace lita.

Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu layika sun karu a gidajen mai na NNPC sakamakon tashin farashin fetur.

Wani jami’in NNPCL a daya daga cikin gidajen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce suna jiran umarnin fara siyar da man kan sabon farashin.

“Mun zo da safiyar yau (Talata) mun kunna injin mu kawai sai muka ga farashin ya canja. Kuna iya gani da idanku. Yanzu muna nan muna jiran umarnin fara siyarwa,” inji shi.

Masu ababen hawa da ke kan layin mai sun nuna damuwarsu kan ci gaban da aka samu.