
Jam’iyyar PDP ta dakatar da Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi kan wasu zarge-zarge na yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa.
Wannan mataki , a cewar wata takarda da jaridar TRIBUNE ONLINE ta gani a yau Juma’a, kwamitin gudanarwar jam’iyyar na gundumar Ayetoro/Iluagba Ward 1 ya yanke shi ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin bincikar laifukan da Melaye ya aikata.
Ga dukkan alamu abubuwan da Melaye ya yi a baya-bayan nan sun saɓawa wa manufofin jam’iyyar PDP da hadin kai, wanda ya sa aka dakatar da shi.