
Tsohon gwamnan Jihar Plateau, Sanata Joshua Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da wasu mutane biyu sun shaƙi iskar ƴanci.
A ranar 14 ga watan Afrilu ne majalisar tsofaffin shugabannin ƙasa, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da yin afuwa ga tsofaffin gwamnonin biyu da ma wasu, matakin da ya janyo cece-kuce a ƙasa.
A lokacin da aka tuntubi Kakakin Hukumar Kula da Gyaran Birnin Tarayya Abuja, Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar wa wakilinmu sakin su a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Karin bayani na nan tafe…