
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar, ya tabbatar da ganin jaririn wata, inda hakan ya nuna cewa gobe Asabar, 2 ga watan Afrilu, za ta zama 1 ga watan Ramadan.
A jawabin ganin watan a kafafen yaɗa labarai kai tsaye, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce Sultan ɗin ya tabbatar da ganin jinjirin watan a wasu garuruwa a nan Nijeriya.
Sarkin Kano ya ce Sultan ya tabbatar da ganin watan a garin Bajoga da ke Jihar Gombe, Kauran Namoda a Jihar Zamfara da sauran jihohi.
Ya ce bayan wannan tabbatar wa, Musulmai za su tashi da azumi, inda watan Ramadan ya zama kwana 1 kenan a goben.
Bayero ya kuma hori al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan dama su yi wa ƙasa addu’a.