
Kotun daukaka ƙara da ke Abuja ta buƙaci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin tarayya da su bi hanyar yin sulhu a wajen kotu domin magance kai-ruwa-ranar da su ke ta yi tsakanin su.
Kotun ta dauki wannan mataki ne a yau Laraba yayin da ta ke sauraron karar da kungiyar ASUU ta shigar kan hukuncin da kotun masana’antu ta kasa ta yanke a ranar 21 ga watan Satumba, inda ta umarci malaman jami’o’in da su dakatar da yajin aikin da suke yi.
Cikakken bayani na nan tafe…