
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Ahmad Sani Kaura ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa ya faɗi ne ya rasu a na tsaka da taro da kungiyar malaman addini a yau Laraba a Gusau.
Wani kusa a jam’iyyar, Aminu Umar ya ce dama marigayin bashi da lafiya, kuma bai warke ba lokacin da ya halarci taron.