Home Labarai YANZU-YANZU: An tabbatar da rasuwar shugaban ƙasar Iran Raisi a haɗarin jirgin sama

YANZU-YANZU: An tabbatar da rasuwar shugaban ƙasar Iran Raisi a haɗarin jirgin sama

0
YANZU-YANZU: An tabbatar da rasuwar shugaban ƙasar Iran Raisi a haɗarin jirgin sama

Shugaban ƙasar Iran,Ebrahim Raisi ya rasu bayan da wani jirgi mai dauke ungulu ya faɗi da shi da sauran jami’an gwamnati a wani jeji mai tsaunuka a cikin ƙasar sakamakon rashin kyawun yanayi.

Raisi, mai shekaru 63 da haihuwa na jagorantar tsagin gurguzu da tsatstsauran ra’ayi na siyasar ƙasar.

Ya shugabanci ƙasar na kimanin shekaru uku kuma na shirin sake tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.

Raisi, wanda tsohon cif joji ne na ƙasar, ana ganin shi zai gaji Ayatollah Ali Khamenei, babban jagora a ƙasar mai shekaru 85.

An haifi Raisi a Mashhad da ke Arewa-maso-Gabashin ƙasar, inda yanki ne na matattarar ƴan Shi’ah.