Home Labarai YANZU-YANZU: Tsohon Sifeto-Janar na ƴan sanda, Tafa Balogun ya rasu

YANZU-YANZU: Tsohon Sifeto-Janar na ƴan sanda, Tafa Balogun ya rasu

0
YANZU-YANZU: Tsohon Sifeto-Janar na ƴan sanda, Tafa Balogun ya rasu

 

 

Tsohon Sufeto-Janar na Ƴan sanda, Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu.

Wata majiya daga iyalan sa ta tabbatar da mutuwar tsohon sufeton yan Sandan, inda ta ce ya rasu yana da shekaru 75.

Tafa Balogun, wanda ya rike mukamin Babban sufeton yan sanda a watan Maris na 2002.

An haife shi a ranar 8 ga Agusta, 1947 a Ila-Orangun a Jihar Osun, Tafa Balogun, shi ne Sufeto-Janar na ‘yan sanda na 21 Kuma ya yi aiki a jami’an ‘yan sanda daban-daban a fadin tarayya, kuma ya samu karin girma kamar yadda ya kamata bayan samun horo, daga Bisani ya kuma kasance kwamishinan Yan sanda a jihohin Ribas da Abia.

Tafa Balogun babban jami’i ne a babbar jami’ar soja a Najeriya, Kwalejin Yaki ta Kasa, daga baya ya zama Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda A.I.G shiyya ta daya, Kano, inda daga nan ne aka nada shi sufeton yan sanda na 21 a ranar 6 ga Maris, 2002.

A ranar 4 ga Afrilu, 2005, Tafa Balogun ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa laifin sata da kuma karkatar da sama da dala miliyan 100 a cikin shekaru uku da ya yi a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda daga asusun ‘yan sanda.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a karkashin Nuhu Ribadu ta gabatar da tuhume-tuhume 70 a kansa, wadanda suka hada da tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004 a lokacin yana Sufeto Janar na ‘yan sanda.

Bayan tafka sharia agaban kotu daga Bisani yayi ikrarin mayar da mafi yawan kadarorin da kudaden. An yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.