Home Siyasa YANZU-YANZU: Da yiwuwar APC ta hukunta Tinubu bisa kalaman da ya furta kan Buhari

YANZU-YANZU: Da yiwuwar APC ta hukunta Tinubu bisa kalaman da ya furta kan Buhari

0
YANZU-YANZU: Da yiwuwar APC ta hukunta Tinubu bisa kalaman da ya furta kan Buhari

 

 

 

Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce da yiwuwar jam’iyyar ta hukunta Asiwaju Bola Tinubu kan kalaman da ya yi akan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A lokacin da ya ziyarci Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a ranar Laraba, Tinubu ya shaida wa wakilan jam’iyyar APC cewa ba dan shi ba, da Buhari bai zama shugaban kasa a 2015 ba.

Wannan tsokaci dai ya janyo cece-kuce a fadin kasar nan.

Da ya ke zantawa da manema labarai a shelkwatar jam’iyyar APC da ke Abuja a yau Asabar, Adamu ya ce, “Muna iya hukunta shi (Tinubu) kan kalaman da ya yi akan Shugaban kasa.”

Adamu ya kuma ce babu wani dan takarar shugaban kasa da aka haramtawa tsayawa takara a zaben fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ake shirin yi a ranar Litinin.