
Daga Bashir Muhammad
Hoton Fulani Siddiƙa, wacce ɗiyar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi (Nabiyu) ce, ya ɓulla a kafar sada zumunta ta Instagram da ƙwaryar ciki.

An sha shagulgulan biki a birnin Kano yayin da Fulani Siddiƙa ta auri angonta Umar Kurfi a ranar 23 ga watan Disambar bara.
Hoton wanda kamfanin dauƙar hoto na Atilary Photography ke terere da shi a Internet, ya ja hankalin akasarin mutane zuwa tofa albarkacin bakinsu.
A yayin da wasu ke ganin hoton ya saɓawa ƙa’idar addini, wasu kuma sai sambarka su ke yi Siddiƙa ta yi nauyi.
Sarki Sanusi (Nabiyu) ya kawo zamananci da dama a harkar masaurar Kano. A watannin da su ka gabata an yi ta kace-nace bayan ya tura ’yarsa ta wakilce shi babu lulluɓi a wani taro a Habuja.
Haka zalika an yi ta cece-kuce kwanan baya lokacin da sarkin ya ce ‘yar sa ta tsinkawa mijinta mari duk lokacin da ya sake ya mare ta.
Mene ne ra’ayinku akan wannan hoton?