Home Kasuwanci Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba- Ƙungiyar Ƙwadago

Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba- Ƙungiyar Ƙwadago

0
Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba- Ƙungiyar Ƙwadago
wooden gavel and books on wooden table,on brown background

 

 

 

 

Kungiyar Kwadago ta ƙasa, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da shirin ƙara farashin man fetur a Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja a yau Alhamis.

A cewarsa, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, Mele Kyari, ya sanar da cewa farashin man fetur zai iya yin tashin gwauron zabi har N340 daga watan Fabrairun 2022.

Amma da ya ke maida martani ta sanarwar, Wabba ya baiyana matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na cewa za ta riƙa baiwa ƴan Najeriya miliyan 40 Naira 5,000 a matsayin abin da zai rage musu raɗaɗin illar karuwar farashin man fetur da cewa babu hikima a ciki.

A cewarsa, jimillar kuɗaɗen da gwamnatin ta ce za ta riƙa baiwa ƴan ƙasa ya zarce kuɗaɗen da ta ce ta na kashewa a halin yanzu kan tallafin man fetur.

Shugaban na NLC ya ce duk wani yunƙuri na kwatanta farashin man fetur a Nijeriya da sauran kasashen duniya zai zama kuskure ne, inda ya suffanta yanayin da cewa “kamar ka kwatanta tuffa da mangwaro ne.”

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tuni ƴan ƙasa dai su ke ta tofa albarkacin bakinsu a kan wannan batu na ƙarin man fetur ta kafafen sadarwa.