Home Siyasa Yari ya magantu kan rahoton komawar sa PDP

Yari ya magantu kan rahoton komawar sa PDP

0
Yari ya magantu kan rahoton komawar sa PDP

 

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa shi bai tsayar da matsaya ba a kan jam’iyar da zai koma, duk da cewa ya yanke shawarar fice wa da ga jam’iyar APC.

Yari, ta bakin Shugaban Yada Labaran sa, Ibrahim Birinin Magaji ya ce, batun sauya shekar sa karya ce tsagwaronta.

Magaji ya bayyana matakin da shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya dauka a matsayin riga malam masallaci. “A gaskiya mun yanke shawarar barin APC, mun kuma tattauna da jam’iyyun siyasa da dama, ciki har da PDP, amma har yanzu ba mu kai ga cimma matsaya da wata jam’iyyar siyasa ba.”

“Ko da mun kammala komawa PDP, ro mu ne za mu yi wa ‘yan jarida jawabi kan sabuwar shawarar da muka yanke ba PDP ta yi magana a madadinmu ba,” inji shi.

Tsohon kwamishinan ya ce shugaban PDP, Kanar Bala Mande bai tuntube su ba kafin ya shirya taron manema labarai.

“Mun yi mamakin jin irin wannan furucin daga bakin shugaban jam’iyyar na jiha, alhali ba mu kammala wani shiri ba, kuma babu wata takarda da za ta goyi bayan ikirarin nasa,” in ji shi.

A ranar Lahadi ne Mande, Shugaban Jam’iyar PDP na Zamfara, ya shaida wa duniya cewa tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da Sanata Marafa da magoya bayansu sun koma jam’iyyar PDP a hukumance.