
Yarima Charles mai jiran gadon sarautar Burtaniya tare da kai dakinsa Camilla sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin wata ziyara da suka kawo Najeriya ta musamman.
Shugaban tare da tawagar manyan jami’an Gwamnatinsa ne suka marabci babban bakon a fadar Gwamnati dake Aso Rock Villa a babban birnin tarayya Abuja.