
A yau ake nada Dan takarar Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a matsayin Wazirin Adamawa, Sarauta mafi muhimmanci bayan Lamidon Adamawa.
Bikin ya samu halartar manyan mutane a ciki da wajen kasarnan a fadar Lamidon Adamawa dake Yola babban birnin jihar.