
A yau Lahadi a ke sa ran ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, zai zo Kano domin karɓar Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau tare da jama’arsa zuwa jam’iyar.
Shekarau dai ya bar jam’iya mai mulki zuwa NNPP, amma bayan watanni ƙalilan, sai kuma zaman su da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙi daɗi, inda ya bayyana cewa an masa rashin adalci sakamakon kin mutunta yarjejeniyar raba takara ga mabiyansa a jam’iyar.
Tun da ga nan alamu su ke nuni da cewa Shekarau ɗin, wanda shi ma tsohon Gwamnan Kano ne, zai sake sauya sheƙa zuwa PDP, jam’iyar da ya taɓa yi a baya.
Jaridar Daily Trust ta tabbatar da cewa shugaban jam’iyar PDP a Kano, Shehu Wada Sagagi, ya tabbatar da cewa Shekarau, wanda ke riƙe da kujerar sanata a karkashin NNPP, ya amince da komawa PDP.
“Mun gode Allah cewa yanzu mun samu jagora. Na ji daɗi. Kasancewar sa ya riƙe muƙamin siyasa mafi girma a jihar, Shekarau ya amince zai dawo PDP .
“Tuni an kammala shirye-shiryen tarbar Atiku Abubakar a nan Kano ranar Lahadi, inda mu ke fatan karɓar Shekarau zuwa janiyar mu.
“Mu ma mun amince za mu yi masa biyayya har mu kai ga nasara,” in ji shi.
A tuna cewa tuni PDP ɗin ta rabe gida biyu a Kano tsakanin ɓangaren Aminu Wali da kuma na Shehu Wada Sagagi, inda daukkanin su sun fitar da ɗan takarar PDP.