
Hukumar zaɓe a mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta ce a yau Laraba ne za ta bai wa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa farfesa Kaletapwa Farauta shaidar sake cin zaɓe karo na biyu.
INEC din ta ce za ta bai wa Fintiri da mataimakiyarsa shaidar cin zaɓen ne da misalin karfe 3 na rana.
A jiya Talata ne jami’in sanar da sakamakon zaɓen jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen da ƙuri’a, 430, 861.
Fintiri ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a, 398, 788.
INEC ɗin za kuma ta bai wa ƴan majalisar tarayya da na jihohi da aka zaɓa shaidarsu ta cin zaɓe.